fbpx
Friday, May 14
Shadow

Har yaushe za mu daina rasa rayukan masu daraja a Nageriya – Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya nuna damuwarsa game da mutuwar wasu daliban uku da aka sace a Jami’ar Greenfield.

An bayyana cewa uku daga cikin daliban da aka sace na jami’ar Greenfield, Kasarami Kaduna, an tsinci gawarwakinsu a mace.

Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Atiku, a wani sako da ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana kisan daliban da aka sace a matsayin abin Allah wadai.

Ya kara da cewa har yaushe za mu daina rasa rayukan a Nageriya? Allah ya baiwa danginsu hakuri.

Ya kamata a baiwa Jihohi dama su dauki kwararan matakan kare rayuka da dukiyoyi al’ummominsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *