fbpx
Friday, January 21
Shadow

Hari kan ofishin Barau: Ƴan sanda sun kama mutane 13

Rundunar ƴan sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da kama mutum 13 da ake zargi da ƙona ofishin kamfe na Sanata Barau Jibrin da ke kan titin Maiduguri Road a Kano.

Daily Nigerian Hausa ta rawiato cewa da sanyin safiyar yau Alhamis ne dai wasu gungun ƴan daba, ɗauke da muggan makamai, su kai dirar mikiya a kan ofishin kamfe na sanatan, inda su ka farfasa kayayyaki, tebura, kujeru da allunan kamfe, sannan su ka ƙone wani sashe na ginin.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, kwamishinan ƴyan sandan, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umurci rundunar ‘Operation Puff Adder’ da su kai ɗauki wurin, domin kama masu laifin da bayar da tsaro.

Ya ƙara da cewa da ga jin umarnin na Kwamishinan, nan da nan jami’an ƴan sanda su ka hallara a gurin, inda su ka kama mutane 13.

Kiyawa ya ce jami’an na ƴan sanda ba su daɗe da zuwa ba su ka shawo kan lamarin, inda ya ƙara da cewa sun samu muggan makamai da kayan shaye-shaye a gurin ƴan daban.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da, muggan makamai guda 34, da jarkar da ake zargin man fetur 2 ganyen wiwi guda 30, da tarin kwayoyi 24 da kuma sholisho 4, Wayar Hannu 1, Masoyan rufi 2 da tarin laya.

Kiyawa ya ce tuni rundunar ta yi nisa wajen bincike, inda ya ƙara da cewa da zarar ta gama binciken za ta maka masu laifin a kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *