fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Harin jirgin saman NAF ya kashe ‘yan bindiga da yawa a jihar Neja, yayin da kuma ya kashe wasu mutanen gari dake halartar biki

Wani jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya (NAF) Alpha jet ya kai hari ta sama a kusa da garin Genu na jihar Neja a karshen mako.

Bama-bamai na sama sun kawar da ‘yan bindiga da yawa da ke gudu a cikin ayarin motoci. Hakanan an kashe garken shanun da suka sata.

Daya daga cikin bama-baman da ake zargin ya kauce zuwa wajen bikin aure a wata unguwa da ke makwabtaka da gurin.

Wani ganau ya ce sun ga wani jirgi yana jefa bama-bamai kan ‘yan fashi kuma daya ya sami wasu mutane da ke bikin aure a kauyen Argida.

“An kashe wasu mazauna kauye biyu. Mun tattara cewa wasu da yawa wadanda suka kasance baƙi a wurin bikin auren, sun sami raunuka. ”

Daraktan Watsa Labarai na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ya fada wa PRNigeria cewa hare-hare ta sama da aka kai an samu nasara sosai.

“Ba mu da wani bayani game da duk wani farar hula da ya rasa ransa. Manufarmu ta yakar ‘yan bindiga ne a wannan yankin na Genu, bayan da muka samu bayanan sirri kan munanan abubuwa da ke shirin tsoratar da mutane, “in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *