fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Harin tsoro Iran ta kaiwa Amurka, Ta sanar da Amurkar shirinta: Ji yanda Sojojin Amurka suka tsallakewa harin

Rahotannin dake fitowa kan harin da kasar Iran ta kaiwa Amurka a sansanin sojojinta dake Iraqi na cewa harin na tsorone Iran ta yi, dan kuwa Iran din ta sanar da yin harin kamin ta yishi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Rahotanni daga CBS da CNN sun bayyana cewa Iran ta bari Amurka ta gane cewa zata kai mata Hari da gangan dan ta ga wane irin martani Amurkar zata yi?

Sannan makaman Iran data harba suna daukar lokaci kamin a harbasu,wannan ma ya kara baiwa Amurka damar ganowa da na’urorin leken Asiri cewa ana shirin kawo mata hari.

Hakanan Wani rahoton yace Iran bata yi amfani da mugun makami ba wajan kai harin kuma ta hari wajene wanda tasan cewa ba za taiwa Rundunar ta sojin Amurka illa sosai ba da gangan, rahoton yace da Iran taso ta yi mummunar illawa sojojin Amurkar, tana da babban makamin da zai iya yin hakan amma sai bata yi amfani dashi ba, Kamar yanda hakan ke yawo a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.

Hakanan sojojin Amurka a kasar Iraqi basu da makamin da zai iya tare rokoki  da Iran ta harba musu tunda yaki da ISIS ya kaisu kasar wadda kuma bata da irin wadannan makamai.

Wannan yasa, da Amurkar ta samu sakon Iran na cewa zata kawo mata hari, sai sojojinta suka shiga dakuna na musamman da zasu basu kariya daga harin makamin na Iran, wannan ne yasa ba’a samu asarai ba


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *