fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Hatsarin mota a ranar Sallah akan babbar hanyar Ilorin zuwa Jebba ya lakume rayukan mutane 10

Wani hatsarin mota a ranar Sallah akan babbar hanyar Ilorin zuwa Jebba ya lakume rayukan mutane 10

Hadarin, wanda ya hada da motar bas ta Hiace mai kujeru 18, ya faru ne a wani wuri da ake kira Iyemoja, a cikin Olooru-Oko Olowo, a cikin karamar hukumar Moro ta jihar Kwara.

Hadarin, wanda rahotanni suka ce saurin gudun wuci gona da iri ne ya haifar dashi, ya faru ne da misalin karfe 4 na yamma.

Kwamandan yanki na hukumar kiyaye haddura ta kasa, Jonathan Owoade, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce baya ga mamatan, wasu fasinjoji da dama sun samu raunuka daban-daban.

Ya lura cewa motar kasuwancin tana da lamba, LND 742 XK, ya kara da cewa an kai wadanda suka ji rauni zuwa wani asibiti mai zaman kansa, asibitin Ayo, Oko Olowo, da kuma Babban Asibitin, Ilorin, domin kula da su.

Shugaban hukumar ta FRSC, wanda ya ce an ijiye gawarwakin a dakin ijiye gawarwaki na babban asibitin, ya yaba wa jami’an rundunar ‘yan sanda na Najeriya kan yadda suka taimaka wa hukumar yayin lamarin.

Owoade ya gargadi direbobi da su guji yin sauri, inda ya bukace su da su bi duk ka’idojin zirga-zirgar tare da yin la’akari da sauran masu amfani da hanyar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *