fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 2 a Anambra

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa, FRSC, a Anambra ta ce hatsarin da ya faru a kogin Ekulo a Oraifite, a kan babbar hanyar Owerri-Onitsha ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a daren Laraba.

Kwamandan rundunar, Adeoye Irelewuyi, ya tabbatar da faruwar hatsarin ga manema labarai ranar Alhamis.

A cewar Mista Irelewuyi, motar kirar Toyota Sienna mai lamba ENU 609 CN, ta fada cikin rami.

Ya ce: “Rahoton shaidun gani da ido da ke iso mana yana nuna cewa direban motar da ba a san ko wanene ba yana cikin tsananin gudu lokacin da ya rasa yadda zai yi sannan ya kutsa cikin rami.

“Fasinjoji bakwai ne hatsarin ya rutsa da su, maza biyar manya da mata biyu manya.

“Jami’an FRSC ne suka ceto wadanda suka jikkata sannan aka kai su asibitin Josephine da Lawrence, Oraifite, inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwar maza biyu.”

Ya ce an ajiye gawarwakin mutanen a gidan ajiye gawa na Restland da ke Oraifite.

Mista Irelewuyi, yayin da yake jajantawa da iyalan mamacin, ya gargadi masu ababen hawa kan gudu da hatsarin tuki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *