fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Hausawa dake Jihar Rivers sun koka da cewa Gwamnatin jihar zata rushe musu gidaje

Hausawa dake zaune a Trailer Park dake Eleme a jihar Rivers sun koka da cewa,  gwamnatin jihar na son rusa musu gidaje.

 

Gwamnatin jihar dai ta fara rusau inda take cire dakunan da aka yi ba bisa ka’ida ba dan yakar matsalar tsaro.

 

Gwamnan jihar, Nyesome Wike ya sha cewa, irin wadannan gurare na ajiye masu laifi ne. Saidai shagaban Hausawan wajan, Shittu Dahiru ya bayyana cewa, shekarunsu 37 suna zaune a wajan amma ba’a taba kama wani da laifi aka kaishi wajan ‘yansanda ba.

 

Yace suna neman dauki daga wajan Gwamnan jihar ya ji kukansu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *