fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Hoto: An bankado yadda dalibai ke satar amsa da Takunkumin “facemask

Farfesa a Jami’ar koyar da aikin Gona ta tarayya (FUAM) da ke Makurdi Farfesa Egbe Okpenge tace a yanzu dalibai suna amfani da takunkumin fuska na “facemask” domin yin magudin jarrabawa.

 

Farfesar ta yi wannan bayani ne a lokacin da take gabatar da wata takarda a wajen wani taro na yini guda ga ɗaliban manyan makarantu.

Ta kuma kuma ce ba kasafai ake samun dalibai da ke da dabi’u marasa kyau ba tsakanin samari da ‘yan mata a cibiyoyin karatun.

A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda mahaifin daya daga cikin daliban makarantar Federal College of forestry Kaduna da aka sace ya mutu da takaicin sace diyarsa.

 

Shi ma a nasa bangaren Babban darakta a hukumar wayar da kai ta kasa (NOA), Dr Garba Abari, wanda ofishinsa ne ya shirya shirin, ya shawarci daliban da su rungumi halayen kwarai don bunkasa cigaban kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *