fbpx
Monday, September 27
Shadow

Hoto: Cristiano Ronaldo ya shiga kundin tarihin Duniya

Shahararen ɗan kwallon duniya, Cristiano Ronaldo, ya kafa tarihin shiga littafin bajinta na duniya.

Ronaldo wanda kwanan nan ya koma Man Utd daga Juventus ya kafa wannan tarihin ne bayan zama kan gaba a tarihin ci wa tawaga kwallaye a duniya, bayan da ya zura kwallo biyu a ragar Ireland.

Sai dai an daga masa jan kati sakamakon cire rigar da ya yi a lokacin murna.

Kawo yanzu Ronaldo ya zura kwallaye 111 a raga a tawagar Portugal, ya kuma ɗara Ali Daei na Iran mai bajintar cin 109 tsakanin 1993 zuwa 2009.

Ronaldo ya mika sakon murna a shafinsa na Facebook tare da jaddada muhimmanci ci gaba da nuna kwazo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *