fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Hoto Da Duminsa: Bayan gumurzu da musayar wuta, Sojoji, ‘Yansanda da DSS sun kashe mataimakin Shugaban IPOB da ya shirya kai hari hedikwatar ‘yansanda

Bayan musayar wuta tsakanin gamayyar jami’an tsaron Sojoji, ‘yansanda dana ‘yansandan farin kaya na DSS, sun yi nasarar kashe wani babba a kungiyar IPOB.

Mutumin me suna Ikonso Commander shine babban jami’in IPOB a gaba dayan jihohin Kudu maso Gabas dake shirya hare-hare ciki hadda wanda aka kaiwa baban Ofishin ‘yansanda na jihar Imo da kuma Hukumar Gyara hali.

 

An kasheshi tare da wasu 6 daga cikin mayakansa sannan kuma aka kama wasu daga cikin an kuma kwato Bindigun Ak47 6 da Albarusai da yawa da kuma wasu kayan tsubbu.

 

Vanguard ta ruwaito cewa yanzu haka akwai Soja 1 da ‘yansanda 3 da suke karbar kulawa Asibiti, bayan sun ji raunuka dalilin Artabun.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *