fbpx
Monday, September 27
Shadow

Hoton Dansandan da ‘yan Bindiga suka kashe a Kaduna suka sace iyalansa

‘Yan Bindiga a jihar Kaduna sun kashe wani Dansanda tare da sace iyalansa.

 

Hakanan sun sace karin wasu mutane 20. Lamarin ya farune a Unguwar Maje da Unguwar Laka dake karamar Hukumar Chukun ta jihar.

 

‘Yan Bindigar sun shiga garinne yayin mutane ke bacci inda suka bude wuta kan me uwa da wabi.

 

Dansandan da aka kashe ya dawo gidane ganin iyalansa daga Jihar Rivers inda yake aiki. Hakanan wani tsohon soja ma ya tsallake rijiya da baya yayin harin.

Kakakin ‘yansandan jihar, Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *