fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Hotuna: An kama Matasan da suka hada baki dan sace dan makwabta a Zaria

‘Yansanda a jihar Kaduna sun kama wasu matasa 3 da suka hada baki dan sace dan makwabta a Tudun Jukun dake Zaria.

 

Kakakin ‘yansandan Jihar, Muhammad Jalige ya bayyanawa manema labarai cewa, mutumin me suna Malam Sama’ila ya kai karar cewa an sace masa Da wanda bai san inda aka kaishi ba.

 

Yace wanda suka sace yaron sun kira mahaifin inda suka ce ya kai musu Miliyan 1,500,000 idan yana son ganin dansa. Da aka ci gaba da tirka-tirka dai, sun amince akan Naira Dubu 50.

 

Bayan an saki yaron, ya rika kiran sunan wani Sani Sa’adu wanda makwabcinsu ne, daga baya an kaiwa ‘yansanda Rahoto inda suka kamashi suka fara bincike, kuma ashe shine babban wanda ya jagoranci ta’asar.

 

Akwai kuma Abdullahi Usman da Usman Idris da yace tare suka yi aika-aikar. Yace duka an kamasu kuma suna fuskantar bincike wanda daga baya za’a kaisu kotu.

”In a turn of events, the victim kept calling the name of one Sani Sa’adu who is their neighbor which arose the suspicion that he might know a thing about the incident.

Police immediately intervened and invited the said Sani Sa’adu for questioning. Lo and behold, it was discovered that he is the principal suspect who masterminded the kidnapping incident and went ahead to mention his criminal accomplices as One Abdullahi Usman and Usman Idris all of the same address.

They were both arrested and currently undergoing investigation after which they will all be charged to court as soon as possible.”the police spokesperson revealed

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *