fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Hotuna: An kama mutane 33 da ake zargi da damfarar intanet a Calabar

A ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati, (EFCC), ta cafke wasu mutane talatin da uku (33) da ake zargi da damfara ta yanar gizo a yayin da suka kai samamen a wurare daban -daban a Calabar, jihar Kuros Riba.

An kama mutum goma sha bakwai daga cikin wadanda ake zargin a wani wuri da ke kan titin Post Office, Royal Estate, kusa da Ekot Onin, yayin da aka kama mutum goma a No.1 Marian Owan ta mahadar Lemena. Sauran mutane shida da ake zargi an cafke su ne a Extension Parliament, Calabar.

Wadanda ake zargin yan tsakanin shekarun 22 – 35 sune: Modey Terrence Akong, Detoo Bem Daniel, Godson Topbie, Moses Valentine Nkpung, Idang Confidence, Chinagorom Edward, Enwereuzo Chidiebere, Obioma ThankGod, Richard Reinhard, Clinton Christopher, Raymond Samuel, Etim Paul, Okechukwu Caleb da Joseph Akobo.

Sauran sune Morayo Jerry, Ogar Jemyford, Emmanuel Chika, Okpubeku Prosper, Onedo Caleb, Enajemo Oghenekaro, Great Asume, Ebuka Uzokwe, Obikwelu Ugochukwu, Oloko Pius Monshe, Gideon Ani, Effiong Akaninyene, Agoh Oscar, Agu Favor, Abang Gods, Luka Kaben, Ifeanyi Enwereuzo da Achilonu Moses.

A lokacin da aka kama, an kwato kwamfyutocin tafi -da -gidanka da wayoyin hannu da yawa daga wadanda ake zargi.

Hakanan an kwato daga gare su motoci Lexus saloon guda uku masu lambobin rajista: LAGOS – AKD 56 FQ, ABUJA- KUJ 79 BM da IMO – UMG 956 KU; Toyota Camry da Honda Accord tare da lambobin rajista LAGOS – APP 368FY da OYO – BDJ 476AQ bi da bi.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kuliya da zaran an kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *