fbpx
Monday, September 27
Shadow

Hotuna: An kama ‘yan Bindiga da suka tuba suka ce sun daina satar Mutane na fashi da makami a Katsina

‘Yansanda a jihar Katsina sun kama wasu ‘yan Bindiga masu satar mutane dan kudin fansa da suka ce sun tuba suna fashi da makami.

 

An kamasu suna aika-aikarne a karamar hukumar Ingawa dake jihar.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, SP Isa Gambo yace wanda aka kama din sun ce sun tuba kuma harma suna aiki tare da hukumomi dan bada shawara kan tsaro.

 

Ya kara da cewa, daya daga cikin ‘yan Bindigar,  Abdullahi Mai-Rafi, tun bayan da ya tuba yana aiki ne tare da me baiwa gwamnan shawara kan harkar tsaro.

 

Yace duka wanda aka kama din sun amsa laifukansu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *