fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Hotuna: An kashe kwamandan IPOB/ESN a Imo, an kwato abubuwa masu fashewa 16

Rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta kashe wani kwamanda a rundunar tsaro ta IPOB, Eastern Security Network, da wasu mutum biyu a yayin wani artabu da akayi a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Michael Abattam ya fitar, ta ce’ yan sandan sun samu bayanan sirri na cewa an ga mambobin IPOB/ ESN da aka haramta a cikin wani gida da ba a kammala ba wanda ke cikin kwari a Amaifeke a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo, inda suka shirin sake kai hare -haren kan yan sanda da cibiyoyin gwamnati a jihar.

Abattam ya bayyana cewa a ranar 11 ga watan Satumba, rundunar yan sanda ta fatattaki maboyar kungiyar da ke cikin wani ginin da ba a kammala ba a kwari a Essential Home wanda aka fi sani da “NGBUKA” a karamar hukumar Amaifeke Orlu ta jihar Imo.

Mambobin kungiyar a lokacin da suka ga jami’an ‘yan sanda a maboyarsu sun bude musu wuta. Sai nan take suma jami’an yan sanda suka mayar masu da wuta cikin tsauri, wanda haka yakai su ga nasarar kashe kashe yan kungiyar IPOB/ESN uku, ciki hadda wani kwamandan su mai suna Chidera Nnabuhe, wanda aka fi sani da “Dragon”.

Hakama yan sanda sunyi nasarar damke wasu daga cikin su, yayin da saura suka tsere da raunukan bindinga.

A lokacin jami’an suke bincike a sansanin yan ta’addan sun gano wata akuya da aka yanka, Kananan bindigogi, harsasai, abubuwa masu fashewa 16, bindigogi 3 masu sarrafa kan su da sauransu.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kuma wadanda a ke zargin yanzu haka ana gudanar da tambayoyi kuma sun yi bayanai masu amfani da za su taimaka wa’ yan sanda wajen cafke sauran ‘yan kungiyar su, ciki har da wadanda suka tsere da raunin harsashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *