Tsohon Hadimin gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai da gwamna, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kora daga aiki bayan sukar gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan a wadannan hotunan.
Bayan da ya soki gwamnatin tarayya kuma har hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS ta kamashi, daga baya an sallameshi daga aiki.
Daga nan ne sai ya sanar da ficewa daga Najeriya wanda kafafen yada labarai da yawa suka fassara hakan da komawa kasar waje da zama.
Saidai ya musanta hakan inda yace babu inda ya fadi cewa ya koma kasar wajene da zama, saboda ko da Abuja ya kasa komawa da zama saboda sabon da yayi da Kano, ballantana ma ace ya bar kasar gaba dayanta?
A baya dai ba’a ji wace kasa ce Salihu wanda aka fi sani da Dawisu ya tafi ba, amma a yanzu ya sanar da cewa yana Birnin New York na kasar Amurka.
A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda Dawisu ya fice daga Najeriya.
Enjoy yourself brother #RelocatedToAbroadDawisu #JapaDawisu https://t.co/lHKpJAlDIt
— Olanrewaju Shittu (@shiism1) March 26, 2021
An ga hotunansa yana shakatawa sosai da cin dadi da kuma yawo da wani Abokinsa, kamar yanda ya saka a shafukan sada zumuntarsa.