fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Hotuna Da Duminsa: Jiragen yakin da Kasar Amurka ta kerawa Najeriya sun iso, inda suka sauka a Filin jirgin sama na Aminu Kano

Jiragen yaki samfurin A-29 Super Tucano da kasar Amurka ta kerawa Najeriya sun iso Najeriyar.

 

Jiragen sun saukane a filin jirgin Sama na Aminu Kano dake jihar Kano, da yammacin yau, Alhamis.

Ministan Tsaro, Janar Bashir Salihi Magashi, me murabus da Shugaban Sojojin Kasa, Janar Farouk Yahaya da shugaban sojojin sama ne suka karbi jiragen.

 

Shekaru 3 da suka gabata ne gwamnatin tarayya data kasar Amurka shuka shiga yarjejeniyar kera jiragen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *