fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Hotuna Da Duminsu:An kama babban Bokan dake baiwa ‘yan IPOB sa’a

‘Yansanda a jihar Imo sun kama wani Uzoamaka Ugoanyanwu wanda shine aka yi imanin yake baiwa ‘yan IPOB sa’a a matsayin Bokansu.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Bala Elkana ne ya tabbatar da kamen, yace wani Ezeugo Ordu dan IPOB me shekaru 65 da aka kama ne ya fallasa Inda bokan yake.

 

Yace am kama bokan da wasu da suka tabbatar da hannunsu a kaiwa gidan Gwamnan jihar, Hope Uzodinma hari, yace suna kira ga sauran masu laifi da ‘yan IPOB musamman wanda suka saci makamai daga hannun jami’an tsaro su mika kansu ga hukuma dan samun sassaucin hukunci, idan kuma ba haka ba, za’a yi farautarsu a kamasu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *