fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Hotuna da Jadawalin Manyan Mutanen Arewa da ake zargi suna da hannu a matsalar tsaro

Matsalar hare-haren ƴan fashi a arewa maso yammacin Najeriya na ƙara laƙume rawunan sarakunan gargajiya a yankin.

An daɗe ana zargin sarakunan gargajiya da hannu a kashe-kashe da satar jama’a da ƴan bindiga suka daɗe suna yi musamman a jihohin Zamfara da Katsina.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Zamfara ta sake dakatar ɗaya daga cikin manyan sarakunan jihar kan zargin alaƙa da ƴan bindiga.

Basaraken shi ne ne na uku cikin manyan sarakuna da gwamnatin Zamfara ta dakatar, akwai kuma wasu hakimai da gwamnati ta dakatar.

Tun da farko wani rahoton kwamitin binciken matsalar tsaro da gwamnatin Zamfara ta kafa a 2019 ya ba gwamnatin shawarwari 132 kuma daga cikinsu akwai shawarar tuɓe wasu sarakunan gargajiya biyar da hakimai 33, wadanda kwamitin ya zarga da hannu dumu-dumu cikin al’amarin matsalar tsaron Zamfara.

Gwamnatin Katsina ma ta dakatar da wani hakimi kan zargin alaka da ƴan fashi masu satar mutane da suka addabi jihar.

Sai dai har yanzu babu wani sakamakon binciken kwamitocin da ake kafawa da ya tabbatar da zargin da ake yi wa sarakunan.

Ga jerin sarakunan da aka dakatar kan zargin alaƙa da ƴan fashi:

Sarkin Zurmi

Sarkin Zurmi, Atiku Abubakar shi ne basarake na baya bayan nan da gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar kan zargin alaƙa da kashe-kashen da ‘yan fashin daji ke yi a yankin masarautarsa.

Gwamnatin jihar ta ce Gwamna Bello Matawalle ya kafa kwamatin bincike ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin gwamna Ibrahim Wakkala kan zarge-zargen da ake yi wa basaraken.

An umarci Bunun Kanwa, Bello Suleiman, da ya karɓi jagorancin masarautar nan take.

Dakatar da Sarkin Zurmin na zuwa bayan harin da aka kai a ƙauyen Kadawa da ke cikin mulkinsa inda rahotanni suka ce an kashe kusan mutum 100.

Sarkin Dansadau

Sarkin Dansadau, Hussaini Umar na cikin sarakunan da aka dakatar a jihar ta Zamfara.

A ranar 1 ga watan Yuni gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin kan zargin alaƙa da ‘yan fashi.

Dagacin Dansadau Nasiru Muhammad Sarkin Kudu ya karɓi ragamar masarautar.

Haka kuma Gwamna Matawalle ya kafa wani kwamati da zai binciki sarkin kan zargin da ake masa, ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin sufetun ƴan sandan Najeriya DIG Mohammad Ibrahim Tsafe (mai ritaya)

Sarkin Maru

Sarkin Maru ne basarake na farko da gwamnatin PDP a Zamfara ta fara dakatarwa tare da tuɓe shi kan zargin hannu a matsalar tsaron jihar.

A watan Agustan 2019 gwamnatin Matawalle ta tsige Sarkin Maru Abubakar Chika bisa zargin cin amanar talakawansa kan alaƙarsa da ƴan bindiga masu kashewa da satar mutane.

Gwamnatin Zamfara ta ce ta tsige Sarkin na Maru ne bayan da kwamitin da ta kafa na binciken zarge-zargen hannun sarakunan gargajiya a sata da garkuwa da mutane, ya samu Sarkin ‘da hannu dumu-dumu’.

Gwamnatin ta fara dakatar da basaraken ne kan zarginsa da wasu talakawansa suka yi yana da alaka da masu satar jama’a.

Sai dai ɓangaren sarkin na Maru ya musanta zarge-zargen da ake yi wa basaraken.

Baya ga sarakuna akwai kuma wasu hakimai ko dakatai da aka dakatar waɗanda ake zarginsu da alaƙa da ƴan bindiga.

Dagacin garin Kanoma

Dagacin garin Kanoma a ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara, Alhaji Lawal Ahmad shi ma an dakatar da shi kan zargin alaka da masu sata da garkuwa da jama’a.

Gwamnatin Zamfara ta dakatar da shi ne tare da Sarkin Maru Abubakar Chika a 2019.

Kwamitin amintattu karkashin jagorancin tsohon sufeto janar na ‘yan sanda, Muhammad Abubakar ne ya bayar da shawarar dakatar da hakimin.

Kwamitin ya ce bincikensa ya gano yadda masu garkuwa da jama’a ke amfani da sarkin Maru da kuma hakimin Kanoma wajen biyan kudin fansa.

Dagacin Nasarawa Mailayi

An dakatar da Dagacin Nasarawa Mailayi, Bello Kiyawa, tare da sarkin Zurmi saboda zarginsa da alaƙa da ƴan fashin daji.

Gwamnati ta zargi hakimin da haɗa baki da ƴan fashin daji masu addabar jihar.

Yankin Zurmi da ke makwabtaka da Katsina ya daɗe yana fama da hare-haren ƴan fashi masu satar shanu da mutane

Sarkin Yakin Kanwa da Marafan Bakura

A watan Janairun 2020 ne gwamnatin Zamfara ta dakatar da wasu uwayen ƙasa guda biyu da ke ƙananan hukumomin Bakura da Zurmi.

Gwamnatin ta dakatar da Alhaji Bello Garba Kanwa, Sarkin Yakin Kanwa da kuma da kuma Alhaji Muhammad Bello Yusuf wanda shi ne Marafan Bakura.

Gwamnatin Zamfara ta ce ta dakatar da uwayen kasar biyu ne bisa rashin biyayya da kuma karan tsaye ga shirye-shiryen gwamnati.

Sauran laifukan sun hada da shiga dumu-dumu cikin harkokin siyasa da kuma zargin almundahana da ruf da da ciki da dukiyar al’umma

To amma da yawa na ganin takun saka tsakanin sarakunan da kuma gwamnatin jihar ba ya rasa nasaba da siyasa.

Kuma wannan ya fara tun lokacin da uwayen kasar suka karbi belin wasu tsoffin kwamishinoni a bangaren jam’iyyar adawa ta APC da gwamnatin Bello Matawalle ta tsare bisa wasu zarge-zarge.

A hira da BBC a farkon mako Yusuf Abubakar Zugu ya musanta cewa akwai siyasa cikin dakatar da sarakunan.

Amma jam’iyyar adawa ta APC ko a baya ta fitar da sanarwar cewa ƴaƴanta a jihar Zamfara na fuskantar takura daga gwamnatin PDP mai ci, wani abu da gwamnatin ke musantawa.

Sarkin Fawwa, Hakimin Kankara

A watan Mayun bana ne masarautar Katsina ta dakatar da hakimi kan matsalar tsaron jihar.

An dakatar da Sarkin Fawwa, Hakimin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal, bisa zargin da ake yi masa na alaka da ‘yan fashin daji da suka addabi jihar Katsina.

Masarautar Katsina ta ce ta dauki wannan mataki ne domin jaddada wa gwamnati da al’umma cewa tana goyon bayan yaki da ta’addanci da mahukunta ke yi.

Tuni masarautar ta kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike a kan zarge-zargen da ake yi wa hakimin na Fawwa Alhaji Abubakar Yusuf.

Wasu daga cikin zarge-zargen da ake masa sun hada da hada baki da yan sa kai wajen aikata wasu abubuwa da ba a fito fili an bayyana ba.

Alhaji Mamman Iso, Sarkin Yakin Katsina, kuma sakataren masarautar Katsina, ya shaida wa BBC cewa babu kanshin gaskiya a zargin da wasu ke yi na cewa ana yi wa hakimin bi ta da kulli ne.

Ya ce idan kwamitin da aka kafa ya kammala bincike zai gabatar da rahotonsa wanda za a aika wa gwamnati, sannan idan har an gano cewa bai aikata laifin komai ba za a bayar da umarnin mayar da shi kan kujerarsa nan take.

1px transparent line

Jihar Katsina da Zamfara mai makwabtaka da ita na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka fi fama da matsalolin tsaro da ake alakantawa da yan fashin daji a wannan lokaci.

Ko da a baya mahukunta a wadannan jihohi biyu sun sha daukar matakin korar masu rike da sarautun gargajiya da ake zargin suna hada baki da maharan da suka addabi jama’a ta hanyar kai hare hare garururwa da kuma satar mutane.

Kwamitin da gwamnatin Zamfara ta kafa domin binciken matsalar tsaron jihar a cikin rahoton da ya gabatar wa gwamnati a 2019 ya ce mutanen da aka kashe sanadiyyar rikicin sun bar zawarawa sama da dubu shida bayan marayu dubu 25.

Duk da cewa mahukunta kan ce suna iya bakin kokarinsu don tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki, bayanai na nuna yadda ake samun karuwar hare-hare da satar mutane, abin da ke nuni da cewa har yanzu da sauran rina a kaba.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *