fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Hotuna: Dakarun sojin Najeriya sun kashe Boko Haram da dama

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa, dakarun sojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram da suka ti yunkurin kaiwa Sojojin Harin ba zata.

 

Rundunar sojin Lafiya Dole dake yaki da Boko Haram a yankin na Maiduguri ta samu bayanan harin na Boko Haram tun kamin su kaishi dan haka ta shirya da Jiragen yaki da dakarunta na kasa, kamar yanda sanarwar da Hedikwatar tsaron ta fitar ta shafinta na Twitter ya bayyanar.

 

An sha gumurzune a Gajigana dake karamar hukumar Nganzai ta jihar Borno, An latata motar yaki 1 ta mayakan Boko Haram din inda suka gudu suka bar 2,an kuma kwato makamai da suka hada da bindigu da harsasai, da bamabamai da aka kera da hannu dadai sauransu.

Sanarwar tace rundunar sojin Najeriya ba zata yi kasa a gwiwa ba sai ta kakkabe duk wata matsalar tsaro

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

1 Comment

  • Sani Aliyu Bug

    Allah ka kara dafawa jami’an tsaron ka nuna mana ranar da za’ace boko haram ta zama tarihi a kasashen da sukeda tasiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *