fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Hotuna: Likitocin da Sanata Aliyu Wamakko ya dauko daga Saudi Arabia sun iso Sakkwato domin yiwa jama’a aikin zuciya kyauta

Likitocin da Sanatan Sakkwato ta tsakiya, Aliyu Magatakarda Wamakko ya gayyato daga kasar Saudi Arabia sun iso a Jihar Sakkwato domin yiwa jama’ar Jihar aikin fida ga masu ciwon zuciya kyauta.

Tuni ayarin Likitocin 24 suka isa Asibitin Koyawarwa ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato.

Likitocin zasu kwashe tsawon mako daya domin yin aikin kyauta ga al’ummar Sakkwato a karkashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko

A yau ne ake sa ran Likitocin zasu fara yin wannan aikin ga marasa lafiyan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *