fbpx
Monday, September 27
Shadow

Hotuna: Mayakan Boko Haram 28 da Iyalansu sun mika wuya ga Sojojin Najeriya a Jihar Borno

A wani rahoto da jaridar TheCable ta fitar, rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun tsare mayakan Boko Haram 28/ (ISWAP) da suka mika wuya kwanan nan a jihar Borno.

Kakakin rundunar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

Nwachukwu ya ce maharan sun mika wuya ga sojojin OPHK, wadanda ke sintiri.

Nwachukwu ya lura cewa sojojin na Forward Operational Base (FOB) da ke aiki a kan hanyar BoCobs-Bama sun kuma kama ‘yan ta’adda 20 da iyalansu, wadanda suka mika wuya ga sojoji a kauyen Nbewa suma a karamar hukumar Bama.

A cewarsa, iyalan maharan da suka mika wuya sun hada da manyan mata 15 da yara 26.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *