fbpx
Monday, September 27
Shadow

Hotuna: Mutane biyu sun mutu yayin da ginin coci ya rufta ana tsaka da ibada a Jihar Taraba

Akalla mutane biyu ne aka tabbatar sun mutu bayan wani gini na cocin Holy Ghost da ke Abeda Pave Community, Chachanji Ward a karamar hukumar Takum a jihar Taraba ya rushe yayin da ake gudanar da ibada a ranar Asabar, 11 ga Satumba.

Rahotanni sun bayyana cewa, ginin ya rufta bayan ruwan sama mai karfin gaske da ya dauki sa’o’i da dama.

Mutum biyu da suka mutu sun hada da namiji daya da macce daya, yayin da wasu mambobin cocin suka samu munanan raunuka.

Da yake tabbatar da rahoton, shugaban karamar hukumar, Shiban Tikari, ya ce duk da yana sane da lamarin, amma har yanzu bai ziyarci yankin ba. Ya kuma tabbatar da cewa mutane biyu sun rasa rayukan su a hadarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *