fbpx
Monday, October 25
Shadow

Hotuna: Wani matashi ya yanka dan uwansa dan shekara 14 a jihar Kwara

Rundunar tsaro ta NSCDC reshen jihar Kwara, ta cafke wani lsmail Saliu, dan shekara 25, bisa zargin hada baki da wani boka, don yanka dan uwansa mai shekaru 14, Azeez Saliu, don yin tsafi na kudi.

Kakakin hukumar NSCDC a Kwara, Babawale Afolabi, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 25 ga Satumba a Ilorin ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a Kosubosu, cikin karamar hukumar Baruten ta jihar.

Binciken da rundunar ta gudanar ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun ja mutumin zuwa gona inda ake zargin “dan uwansa na jini, lsmail Saliu shi ne ya yanka sa.

Saidai cikin rashin sa’a jami’an NSCDC sun damke wadanda ake zargi a lokacin da suke kan hanyarau ta dawowa daga gona.

Sanarwar ta kuma ce kwamandan rundunar na jihar, lskil Makinde, ya ba da umurnin a mika wadanda ake zargin ga ‘yan sanda don ci gaba da bincike da gurfanar da su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *