fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Hotuna: Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe mutane biyar a wani sabon hari da aka kai wa al’umman Benuwai

Wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai hari a wasu kauyuka hudu da ke karamar hukumar Gwer-West ta jihar Benuwai inda suka kashe mutane biyar.

An bayyana cewa wasu mutane uku da suka hada da mace mai ciki sun ji rauni a harin wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Juma’a, 30 ga Afrilu.

Saidai Makiyayan sun tsere da raunin harbin bindiga bayan da sojojin Operation Whirl Stroke (OPWS) suka bi su zuwa kan iyakar Benue da Nasarawa suka yi musayar wuta da su.

A cewar rahotanni, makiyayan sun fara mamaye Kauyen Ahume da ke kan hanyar Makurdi / Naka amma sai sojojin suka fatattake su daga nan kuma suka girka a ƙauyen don guje wa yiwuwar kai harin daga maharan.

A halin yanzu an kwashe gawawwakin yayin da wadanda suka samu raunuka kuma aka kai su asibiti don yi masu magani.

Kalli wasu hotuna a kasa;

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *