fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Hotuna: Wata budurwa ta kashe saurayinta sannan itama ta kashe kanta bayan da ta ji ance zai auri wata

Ana zargin wata Budurwa da kashe kanta da kuma tsohon Saurayinya bayan da ta samu labarin cewa zai auri wata.

 

Mutumin dan Shekaru 34, Akuma Felix Emeka dake jihar Imo ana zargin tsohuwar Budurwarsa da zuba masa guba ya sha ya mutu ana saura mako daya a daura masa aure.

 

An ruwaito cewa, tsohuwar budurwar tasa ta gayyaceshi ne zuwa shan lemu, ashe be sani ba ta zubawa lemun guba. Lamarin ya faru ranar Asabar, 3 ga watan Afrilu.

 

Babu tabbacin abinda ya faru tsakaninsu amma wata majiya ta bayyanawa Igbere TV cewa budurwar ce ta zuba musu guba duka suka mutu. Daga baya an ga gawarwakinsu a cikin motar sa hadda sauran lemun da suka sha.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *