fbpx
Friday, May 14
Shadow

Hotuna: Wata yarinya ta sake haduwa da mahaifiyarta shekaru 20 bayan anyi fataucinta a Jihar Akwa-Ibom

Murna ta barke a tsakanin mutanen Idu Uruan a jihar Akwa Ibom yayin da aka ceto ‘yarsu, wacce akai fataucinta shekaru ashirin da suka gabata.

Anyi nasarar ceto yarinya ta hanyar hukumar NAPTIP tare da haɗin gwiwar IOM.

Wata mata ce ta dauke yarinyar tun tana yar shekaru 6 daga Idu Uruan zuwa Benin City.

A yayin taron, Darakta Janar na NAPTIP Imaan Suleiman-Ibrahim wanda ya samu wakilcin kwamandan shiyyar NAPTIP Benin Zonal Command, Misis Ijeoma Esther Uduak, ta sake nanata kudurin DG na kawar da Fataucin Bil Adama, cin zarafi da cin zarafin kananan yara.

Da yake mayar da martani, Shugaban Kauyen Idu Uruan, Etenyin Obong Godwin Okoho a madadin jihar ya nuna matukar godiyarsa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Darakta Janar na NAPTIP da kuma dukkan shugabannin Hukumar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *