fbpx
Monday, September 27
Shadow

Hotuna: Yan sanda sun cafke wani mai walda wanda ya kware wajen kerawa da sayar da bindigogi ga masu aikata laifuka a Jihar Akwa Ibom

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom sun cafke Ekike Hector David wanda ake zargin yana kerewa yan ta’adda bindigogi.

Kakakin rundunar, SP Odiko MacDon, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 14 ga Satumba, ya ce wanda ake zargin, mai aikin walda ya ƙware wajen ƙerawa da sayar da bindigogi na cikin gida ga masu aikata laifi.

A ranar 13 ga Satumba, 2021, da misalin karfe 1 na rana, tawagar masu sa ido na ‘A’ Division da ke kan titin Barracks, yayin da suke gudanar da bincike na yau da kullun don dakile ayyukan masu laifi a hanyar Uyo Village da kewaye, sun kama Ekike Hector David na Mbiokporo a Karamar Hukumar Nsit Ibom tare da bindigogin AK47 guda takwas da aka kirkira a cikin gida,

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin, mai walda ne wanda ya kware wajen kerawa da sayar da bindigogi na cikin gida da sauran muggan makamai ga masu aikata laifuka wadanda suke amfani da irin wannan wajen tsoratar da jama’a da ba su ji ba su gani ba.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Amiegheme Andy ya ba da umarnin yin cikakken bincike da nufin kama wadanda yake sayar wa bindigogin idan ya kera.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *