Wani matashi da matarsa wanda duka sun kammala karatun Jami’a, Hamza Alkali Kolo da Hauwa Usman sun samu karuwar ‘ya’ya 4.
Lamarin ya farune a Bida dake jihar Naija a babban Asibitin Bida. An rada musu suna ranar 22 ga watan Maris a Masallacin Ummu Amara.
Hamza yayi Karatun injiniya a kwalejin kimiyya dake Bida yayin da matar ta yi karatun kiwon Lafiya amma dukansu babu wanda ke aiki.
Masu hannu da shuni ciki hadda matar gwamnan jihar, Hajiya Amina Abubakar Sani Bello sun tallafa musu da kudi da kayan Abinci da kayan Jarirai.
A baya, hutudole.com ya kawo muku Rahoton yanda Wani magidanci yayi aika-aika akan matarshi yayin da diyarsu ke kallo