fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Hotuna: An Yi Nasarar Kashe Wata Dorinar Ruwan Da Ta Jima Ta Barna A Jihar Kebbi

Mutenan garin Samanaji dake karamar hukumar Koko/Besse a jihar Kebbi sun kashe wata dorinar ruwa a jiya Lahadi 9/2/2020, inda suka dauki tsawon yini suna fafatawa da dorinar, hakan ya samu a sali ne sanadiyar barna da dorinar take yi musu. 

Rahotanni sun bayyana cewa Dorinar ta taba nutsar jirgin ruwa guda hudu kuma tana yi musu barna a gonakin shinkafa.

Shugaban karamar hukumar Koko/Besse, Honarabul Yahaya Bello Koko tare da mataimakinsa Honarabul Umar Musa Besse da uban kasar Dutsin Mari Alhaji Mu’allade da Manu Sule Koko kansilar Magaji da dai sauran al’ummar yankin Koko/Besse, sun samu ziyartar garin Samanaji domin yi wa al’ummar yankin jaje, bisa ga irin barnar da wannan dabbar ruwa ta yi musu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *