fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Hotuna:An karrama ‘yansandan da suka ki karbar cin hancin Miliyan 1 a Kano

Hukumar ‘yansandan Jihar Kano da kuma ta kare masu sayen kayayyaki ta karrama wasu ‘yansanda 2 da suka ki karbar cin hancin Naira Miliyan 1 a Kano.

 

An baiwa ‘yansansan kyautar Miliyan 1 saboda wannan bajinta tasu.

 

Yansandan sune Garba Rabo da Jamilu Buhari wanda ke aiki da hukumar ta CPC, Kakakin ‘yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an labartawa ‘yansandan wani wajan ajiyar kaya da suka lalace inda kuma suka kai samame.

 

Saidai me kayan yayi kokarin basu cin hancin Miliyan 1 amma suka ki karba, suka kamashi da kayan nashi da kuma kudin da ya basu a matsayin cin hanci.

 

Kwamishinan ‘yansandan jihar, Sama’ila Dikko ya jinjinawa ‘yansandan inda ya jawo hankalin abokan aikinsu da su yi koyi dasu.

 

A baya hutudole.com ya ruwaito muku cewa, ‘Yansanda sun kama Aljanu masu damfarar mutane a Katsina

The task force team stormed the warehouse, where one million naira was offered to them as a bribe. They rejected the bribe, recovered the expired goods worth billions of naira, the money as an exhibit and arrested the suspect,” Mr Kiyawa said.Hukumar

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *