fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Hotunan birnin da tafi kowane kazanta a Africa

Babban jami’in ƙungiyar Tarayyar Turai a Laberiya ya ce ya kaɗu matuƙa da yadda babban birnin ƙasar Monrovia yake da datti da ƙazanta, duk da ɗumbin tallafin da ake bayarwa don tsaftace birnin da inganta rayuwa.

Laurent Delahousse ya shaida wa wani taro da Hukumar Birni Ta Monrovia ta shirya cewa ya yi mamaki da abin da ya gani shekara ɗaya da ta gabata lokacin da ya isa birnin.

“Monrovia ƙazamin birni ne, mara dadin zama, mai cike da ƙazanta,” a cewarsa.

“A cikin dukkan biranen da na gano a ƙasashen da na yi aiki a Afirka, ban ga mai datti kamar naku ba,” yaƙara da cewa.

Ya yi kira ga jami’ai da su magance lamarin, su kuma yi bayanin kuɗaɗen da suke samu daga masu ba da tallafi da harajin da suke karɓa daga ƴan kasuwa.

“Tsaftataccen birni kadara ce; yana iya kawo ayyukan yi kuma wannan shi ne abin da Laberiya ta fi buƙata,” a cewarsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *