fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Hotunan wanda ya tsinci Dubu dari biyar ya mayarwa me kudin Abinshi: Sarkin Musulmi ya masa kyautar Kwatankwacin kudin

Me alfarma sarkin Musulmi,  Alhai Abubakar Sa’ad na III ya yiwa wani me tukin keke Napep kyautar Naira 500,000.

 

Mutumin dan kimanin shekaru 40 dake tukin Keke Napep a Jos ya tsinci kudin 500,000 kuma ya nemi me kudin ya mayar masa da kayansa.

 

Ko da sarkin Musulmi ya samu Labari, sai ya aika masa da kyautar wata 500,000 din tare da jinjina masa da kuma fadar cewa haka ake son ganin musulmi na kwarai.

Me martaba sarkin Wase, Sambo Harunane ya mikawa mutumin kyautar da jinjinar a madadin sarkin Musulmi.

 

Yace mutumin abin a jinjina masa ne kwarai da gaske saboda daukakar da ya kara jawowa addinin Islama.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *