fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Hotunan yadda wata halitta me rabi mutum rabi tsuntsu ta addabi wani kauye

Lamarin ya faru a kauyen Pount Pleasant dake Virginia kasar Amurka. Saida aka shafe shekara guda ana ganin wannam Halittar a garin.

 

Kuma sama da mutane 100 ne suka tabbatar da cewa sun ga halittar da idansu, mutane 46 ne halittar ta kashe kamin daga baya a daina ganinta.

 

Shekaru sama da 50 kenan da faruwar lamarin inda amma har yanzu masu bincike ke son gano ainahin abinda ya faru. Lamarin ya faru a shekarar 1966.

Binciken da ake akan halittar wadda aka bayyana me jajayen Idanu ana son gano shin gargadi ta zo yi, shaidaniya ce ko kuwa ta kirki ce, ko kuwa dai babu itama a Zahiri?

 

A Rahoton da Daily star UK ta ruwaito tace zuwa yanzu dai ba’a gano ainahin meme ya faru a garin ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *