fbpx
Monday, September 27
Shadow

Hotunan yanda ake cin zarafin Musulmai a kasar India

Hare-haren ba gaira babu dalili da mabiya addinin Hindu ke kai wa Musulmai a Indiya na kara zama ruwan dare, sai dai kuma idon hukumomi ya fara kai wa gare su a baya-bayan nan.

A watan da ya gabata, wani hoton bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda wata yarinya karama ke rike da mahaifinta Musulmi wanda mabiya addinin Hindu suka ci zarafi.

Bidiyon mai tayar da hankali ya nuna mutumin dan shekara 45 wanda ke jan keken haya ana jan sa a kasa a kan titin Kanpur, wani birnin da ke arewacin jihar Uttar Pradesh, lokacin da yake kuka ‘yarsa na rokon mabiya addinin Hindun su daina dukansa.

Wadanda suke dukansa suna ta ihu suna cewa sai ya ce “Hindustan Zindabad” ko kuma “Long Live India” ko kuma ya ce “Jai Shri Ram” da “Victory to Lord Ram” – wata fitacciyar gaisuwa da suka mayar wani yaren kisa a baya-bayan nan.

Ya fadi abin da suka nemi ya ce, amma duk da haka suka ci gaba da dukan shi. Amma daga baya ‘yan sanda sun ceci mutumin da kuma ‘yar tasa.

Mutane uku da aka kama saboda wannan laifi an sake su kwana guda bayan faruwar lamarin.

Kwanaki kadan bayan haka, sai wani bidiyon da ya nuna yadda mabiya Hindu suka kifa wa wani Musulmi mai sayar da awarwaro mari, suka rika yin bal da shi a birnin Indore.

An rika jin masu dukansa suna zagin sa da sunansa Tasleem Ali, kuma suna ce masa ya kiyayi duk wani yanki na mabiya addinin Hindu a nan gaba.

Amma a karar da aka shigar wajen ‘yan sanda, ya yi zargin “mutum biyar zuwa shida sun dake shi wadanda suka yi masa habaici a wajen kasuwancin da mabiya addinin Hindu suka yi yawa, ya kuma ce an kwace masa kudi da wayarsa da wasu takardunsa”.

Amma a wani abu da ba a saba gani ba, an kama Ali bayan da wata yarinya ‘yar shekara 13 wadda ‘yar daya daga cikin wadanda suka doke shi ce ta zarge shi da cin zarafinta.

Iyalinsa da kuma makotansa sun musanta wannan zargi matuƙa. Suna cewa abun da ba zai yuwu ba ne a karbi wannan zargi daga daya daga cikin wadanda yake rikici da su.

Wani shaidar gani da ido da wata jaridar Indiya ta ambato, ta ce an kai wa mutumin hari ne saboda addininsa, kuma zargin da ake yi masa na cin zarfin yarinya ba shi da tushe.

Wadannan hare-hare biyu na cikin abubuwan da suka faru na nuna kin jinin Musulunci a watan Agusta, amma wannan na nufin mummunan yanayi ga mabiya addinin da su ne tsirari, wadanda suke da adadin mutane kimanin miliyan 200.

An kai kwatankwacin irin irin wannan hare-haren watannin da suka gabata – wasu da dama sun fito fuskar jaridun kasar.

“Rikicin ya mamaye ko ina. Abu ne gama gari kuma da aka amince da shi cikin al’umma,” in ji Alishan Jafri, wani dan jarida mai zaman kansa wanda yake tattara rahoton hare-hare kan Musulmai a India sama da shekara uku baya.

Ya ce a kullum yana “ganin bidiyo uku zuwa hudu” amma bai fi biyu zuwa zuwa daya yake iya tantancewa ba, su ne wadanda yake dorawa a kafafen sada zumuntarsa.

A 2019, wani shafi da yake bibiyar yadda ake aikata laifuka ya ruwaito cewa sama da kashi 90 cikin 100 na wadanda ake cin zarafi Musulmai ne.

Mafi yawan wadanda suke kai hare-haren suna tafiya haka ba tare da an hukunta su ba, lokacin da ake zargin cewa mutanen na samun goyon bayan siyasa daga jam’iyya mai mulki ta Shugaba Modi.

“Irin wadannan hare-haren na kara zama ruwan dare a kasar kuma babu abin da ake yi musu saboda kariyar da ake ba su,” in ji Hasiba Amin, mai kula da kafafen sada zumuntar jam’iyyar adawa ta Congress.

“Yau wannan tsanar da ke tsakanin mutane ta wuce yadda ake zato. Ba wani abu ba ne a kai hari kan Musulmai. Sau da yawa ma a kan bai wa masu harin kyauta kan abin da suka yi.”

Masu suka sun ce tun bayan da Modi ya dawo kan mulkin kasar a 2019, sai masu kin Musulmai suka kara fadada ayyukansu.

A waus lokutan ma, cin zarafin ba na zahiri ba ne a boye ake yinsa, cikin muzgunawa tsirarun al’ummomin.

Mata Musulmai ma ba su tsira ba – a watan Yuli ma, an yi musu wani cin zarafi na sanya hotunan gwammai a intanet ana gwanjonsu.

A watan Mayu, da yawansu ciki har da Ms Amin ta Jam’iyyar Congress, an yi musu wulakacin ta hanyar tallata su a intanet.

Sannan a watan da ya gabata, wasu masu gangami da shugaban BJP na Delhi ya shirya, sun yi ta ihu da kira cewa a kashe Musulmai.

Farfesa Aeijaz ya ce harin da ake kai wa kan Musulmai masu sana’o’i kamar teloli da masu sayar da kayan marmari da masu gyaran lantarki da masu gyaran famfo, kokari ne na kwace iko da ayyuka da tattalin arzikinsu.

BBCHAUSA.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *