A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta raba kayayyakin tallafi na miliyoyin nairori ga al’ummomin da ambaliyar ta shafa a shekarar 2020 dake karamar hukumar Uzo Uwani ta Jihar Enugu.
Kayayyakin agajin, wadanda suka hada da kayan abinci da sauransu.
Hukumar ta rarraba kayan ne zuwa garuruwa uku da suka hada da Ojor, Ogurugu da Igga.
Da yake magana a garin Ojor, Kodinetan NEMA na yankin, Mista Fred Anusim, ya ce ambaliyar ta lalata gonaki da gine-gine da dama a yankunan tun a ranar 3 ga watan Oktoban shekarar bara data wuce 2020.