Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da wani talla a WhatsApp da ake zargin suna neman daukar matasa ‘yan Najeriya cikin hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
Shugaban sashen yada labarai na hukumar ta EFCC, Mista Wilson Uwujaren a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce aikin tallar ya kasance aikin masu damfara ne, in ji NAN.
Uwujaren ya bukaci masu neman aikin da su bi ahanhali kar su fada tarkon damfara.
Uwujaren ya nuna cewa ana sanya tallace-tallace don daukar ma’aikata a cikin hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kan manyan kafafen yada labarai da kuma dandalin sada zumunta na hukumar.
Ya bukaci jama’a da su yi watsi da sakonnin fadakarwa na yaudara da ake zargin hedkwatar hukumar ta EFCC ta bayar a Jabi, Abuja.
Kakakin ya kara da cewa, “Ire-iren wadannan sakonnin ba daga EFCC suke ba tunda hukumar ba ta da‘ sashin taimako, ’