fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Hukumar EFCC Ta Kai Samame Gidajen Sanata Shehu Sani Dake Abuja

Jami’an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC sun kai samame a ranar Laraba gidajen Sanata Shehu Sani a Abuja.

Shehu Sani wanda tsohon sanata ne mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya shafe kimanin kwanaki tara a tsare inda hukumar ke zarginsa da karbar ”kudade da sunan mukaddashin hukumar EFCC Ibrahim Magu”.
Suleiman Sule wanda wani mai taimaka wa Sanatan ne ya shaida wa majiyar BBC cewa jami’an sun shafe kimanin awa daya suna bincike a layin Negro Crescent da ke Unguwar Maitama Abuja.
Haka zalika ya shaida mana cewa jami’an sun shafe kimanin awa daya da mintuna talatin suna bincike a gidansa da ke layin Casablanca da ke Unguwar Wuse II da ke Abuja kuma sun yi awon gaba da katuna na adreshi wadanda aka fi sani da ”complementary cards”.
Bayan haka jami’an sun je ofishinsa da ke layin Monrovia a Unguwar Wuse II inda a nan ma suka gudanar da bincike.
Sule kuma ya tabbatar da cewa har yanzu Sanata Sani yana hannun hukumar ta EFCC.
Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren ya shaida cewa ba da dadewaba zai fitar da sanarwa dangane da binciken da suka yi.
Tun a ranar biyu ga watan Janairu hukumar ta EFCC ta samu amincewa daga kotu kan tsare sanatan kan zarge-zargen da take yi masa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *