fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Hukumar EFCC ta kama wani Uba da dansa bisa zargin zamba ta intanet

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama wani uba, Isa Bola Bakare, da dansa, Malik Giles Bakare a kan zargin hada baki da damfara mai nasaba da kwamfuta.

An kama su ne saboda zargin su da karbar kudi ta hanyar yin karya da kuma rike kudaden haramun.

Jami’an ‘yan sandan Nijeriya, CID, Alagbon ne suka cafke Malik a Legas a ranar 31 ga Mayu, 2021, suka kuma mika shi ga hukumar EFCC.

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya ce Malik ya yi aiki a matsayin “dan tsakiya”.

“Yana hada masu damfarar intanet a duk duniya tare da masu tsinkaye, kuma yana karbar wasu kaso kan kowace ma’amala da ta yi nasara”.

Yayin binciken farko, mahaifin ya bayyana a gaban EFCC kan motar Range Rover ta miliyan N46 da aka kwato daga Malik.

Uwujaren ya ce an kama babban Bakare ne bayan ya kasa bayar da gamsassun bayani kan yadda ya same ta.

Kayayyakin da aka kwace daga wadanda ake zargin sun hada da abin hawa, iphone 12 Pro Max, iphone 8 da “wasu abubuwa masu laifi”.

Za a gurfanar da uba da dan a kotu bayan an kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *