fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Hukumar EFCC ta kama wasu mutane 24 da ake zargi da damfara ta hanyar Intanet a Ogun

Jami’an Ofishin shiyyar Legas na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati, EFCC, sun kama mutane 24 da ake zargi da damfara ta hanyar intanet a jihar Ogun.

 

Hukumar a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a ta ce an cafke wadanda ake zargin ne a gidajensu daban-daban da ke yankin Sango na Jihar Ogun, a ranar 21 ga Maris, 2021, bayan rahotannin sirri da Hukumar ta samu game da shigarsu cikin aikata laifin da ake zargi.

 

A baya dai, hutudole.com ya kawo muku Rahoton yanda wasu ‘yan Bindiga suka Sace wata mata a Jos

 

Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da manyan motoci, wayoyin hannu daban-daban, kwamfutar tafi-da-gidanka, Wi-Fi da na’urorin zamani.

 

EFCC ta kara da cewa nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *