fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Hukumar EFCC ta mamaye otal din Legas, ta kuma kame mutane 30 da ake zargi da zamba

Jami’an hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa sun damke wasu mutane 30 a yayin wani samame da suka kai Otal din Parktonian a yankin Lekki da ke jihar Legas.

An yi zargin cewa jami’an sun sami shiga cikin dakunan mazauna ta hanyar kwace katunan da ke kula da otal din a dakin tarbon baki.

An tattaro cewa wasu daga cikin mutanen sun kasance tsirara a lokacin da jami’an suka samu shiga cikin dakunan.

Daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, yayin da yake nuna bakin cikin sa game da samamem, ya fada wa jaridar Gazette, “Koda suka riskeni nayi tsirara, kuma dole ne na roke su barni na rufe jikina. A zahiri ni mai hawan jini ne, amma hankalina a kwance yake domin kuwa ni ba mai laifi bane. ”

Wani ganau ya ce ga littafin, “Sun kutsa cikin otal din kuma sun yi barazanar harbe masu karbar baki da ma’aikatan gudanarwa idan ba su gaggauta sakin musu katin shiga ba. Don haka, dole ne ma’aikatan otal din suka yi biyayya nan take. ”

A cewar jaridar, an gano cewa baƙi 13 ne suka ɓace daga hannun jami’an EFCC yayin samamen.

Daga baya Wilson Uwujaren, mai magana da yawun EFCC, ya tabbatar da samamen a cikin wata sanarwa.

Ya ce jami’an sun yi aiki ne a kan bayanan sirri da suka samu akan wadanda ake zargi a Otal din Parktonian, ya kara da cewa an kama mutane 30 da ake zargi a yayin samamen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *