fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kwace motoci 2 dauke da giya iri-iri

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kwace motoci biyu dauke da katan 5,760 na giya iri daban -daban a kan hanyar Kano/Madobi.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Lawan Ibrahim-Fagge, ya fitar a Kano ranar Laraba.

Sanarwar ta nakalto kwamandan hukumar, Dr Harun Ibn-Sina yana cewa, yayin da yake duba motocin a hedikwatar hukumar, cewa jami’an Hisbah sun damke su da misalin karfe 4:00 na safe. ran laraba.

“Hukumar Hisbah ta hana sayar da giya a jihar don gujewa maye,” in ji shi.

Ibn-Sina ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da yaki da miyagun kwayoyi da sauran abubuwan maye a tsakanin matasa a jihar.

Ya yaba da kokarin hukumar Hisbah, masu sa kai da masu ruwa da tsaki kan jajircewar su, ya kara da cewa rashin kyawun dabi’a tsakanin matasa ya kasance abin damuwa ga al’umma.

Kwamandan ya ce za a ci gaba da kokarin kawar da al’umma daga barazanar miyagun kwayoyi da sauran abubuwan sa maye.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *