fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Hukumar Hisbah ta Kano ta kame wasu maza 2 saboda tura wa matar aure bidiyon batsa

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da tura wa matar aure bidiyon batsa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Lawan Ibrahim, ya fitar a ranar Litinin a Kano, ta ce an gano wadanda ake zargin tare da kame su bayan matar ta shigar da kara ga hukumar.

Matar ta sanar da jami’an hukumar cewa ana turo mata bidiyon amma ba ta san wanda ya turo sakon bidiyon zuwa wayarta ba.

Nan Babban Kwamandan hukumar, Haruna Ibn-Sina, ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin, kuma akayi nasarar cafke su ta hanya bibiyar lambobin wayoyin su.

Bayan sasantawa, Hukumar tayi kira ga iyayen su domin su ja kunne ya’yanasu, tare da kula da tarbiyar su yanda ya kamata.

A karshe Hukumar ta shawarci iyaye da su guji siya wa yaransu wayoyi masu tsada kuma a koda yaushe su lura da zirga-zirgar su don kare su daga cudanya da miyagun abokai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *