fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Hukumar HISBAH ta Kano ta kori jami’inta da aka zarga da ganinsa da matar aure a dakin Otal

Hukumar HISBAH dake Jihar Kano ta sanar da korar wani jami’inta, da aka zarga da ganinsa da matar aiure a Otal na unguwar Sabon Gari.

 

A ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar 2016 ne dai labarin ya bayyana.

 

Saidai ranar 10 ga watan Maris, Kakakin Hisbah, Nabahi Usman ya bayyanawa Sahara Reports cewa bayan Bincike an wanke jami’in Hisban daga zargin da ake masa inda aka gano cewar matar da ake zargin ganinsa da ita, diyarsa ce.

 

Saidai Lawal Fage wanda shine kakakin hukumar ya sanar da Vanguard cewa an kori ma’aikacin.

 

Hakan ya biyo bayan Rahoton da kwamitin da aka baiwa Alhakin bincike kan lamarin ya tanada.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *