fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Hukumar Karota Ta Yi Rusau A Kasuwar Waya Ta ‘Farm Center’ Dake Kano

A daren Juma’ar da ta gabata ne ‘yan kasuwar waya ta Farm Center dake Kano suka budi ido da ganin rusau a ‘yan tebura dake kasuwar. Inda Hukumar Karota karkashin Bappah Babba Dan Agundi suka kaddamar da rusan yadda duk wani tebur dake gurin ‘yan kasuwar tsayen saida aka yi tafiyar ruwa da shi.

A cewar wani mazaunin kasuwar ya bayyana cewa abinda Gwamnatin ta yi kwata kwata bai dace ba. Ya ce kamata ya yi kafin a rusa musu gurin cin abinci a samar musu da abinda za su yi.
Andai yi wannan rusan ne a gurin masu tsaiwa agun domin saida waya da kuma yan tebura da wasu shaguna da Akai a gun domin saida Caza  da Takalma a kan titin daya ratsa ta Kasuwar ta Farm Center.
To Saidai a zantawar Jaridar Jakadiya da Kakin Kasuwar Jamilu Bala Gama ya shafadi cewa dama aikin hukumar Karota shine buda titunan da aka rufe ta hanyar zama akansu ko kasa wasu abubuwa yace kamar yadda kowa yasani Hukumar Karota ta shigo Kasuwar a Daren jumaa inda tai rusan yace kuma inka duba shi Bappa ba iya Farm Center yai rusan ba yayi a kwari da kurmi da wambai
Ya ce kafin zuwansa Farm Center ya kawowa tsohon Shugabanci na kasuwar Notice na wata guda kan cewa jamaar dake kasa kaya agun su matsa to Cikin ikon Allah har wata ya kare baa matsa ba nan Baffa ya kara aiko da Notice na Sati Biyu to alokacin Mu mun karbi Shugabancin Kasuwar munje mun sameshi ya shaida mana cewa matsayin mu na sabbin Shugabanni ya kara mana sati biyu.
Yace sati biyu ta kammala bamu gama gyare gyaren tashin ba muka kara rokarsa kuma ya kara Mana sati biyu daya bamu munci gabada gyare gyare har mun samarwa mutane tinda zasu koma wato wata Kasuwa da mukeda iya itama ta Gwamnati CE ana kiranta Kasuwar Dan Fulani.
Da wasu makotan kasuwannin mu mun samarwa mutane wuri har sun fara tashi sai wani daga Cikin tsohon Shugabanci Yaje yace musu su dawo Ai tashin da Akai musu ba Na Gwamnati bane to nan mutane kansu ya kulle suka fara dawowa Tinda ai Gwamnati ta tsaheka wani shi kadai yace ka dawo kuma ka dawo bayan kaiwa kasan ba bisa kaida ake zaune ba.
Yace to wannan shiya harzuka Baffa ya zo cikin dare ya yi rusau tin daga bango har karshen bango ta Kasuwar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *