fbpx
Monday, May 10
Shadow

Hukumar Kwastam Ta Kama Kwantina Makare Da Kwayoyin Kodin Da Tramadol

Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen yankin Apapa, a ranar Litinin ta cafke wata kwantena mai kafa 40 makare katan 805 na kodin da kuma katan 127 na tramadol a Legas.

Kwantenan da aka gano a tashar rukunin SIFAX an sanya shi don dubawa lokacin da aka kama shi sakamakon bayanan da ma’aikatan SIFAX suka bayar.
Kwantenar mai tsawon kafa 40 mai lamba : TEMU 6164202 an ce ta kasance karkashin kulawar Kwastam na wani dan lokaci, amma daga karshe “an yi bincike sai aka gano ta dauke da magungunan.”
Ba a san hakikanin darajar haramtacciyar kwayar ba kamar a lokacin a ranar Talata, amma jami’an kwastam da ba sa son a ambaci sunayensu sun sanya darajar titi na magungunan sama da Naira miliyan 500.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *