fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Hukumar NDLEA ta cafke dillalan dake safarar miyagun magunguna zuwa Arewacin Nageriya

Jami’an hukumar hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun cafke wasu manyan kungiyoyin fataucin miyagun kwayoyi guda uku da ake zargin suna ba da haramtattun abubuwa ga wasu jihohin arewacin kasar.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Talata cewa an kama mutane bakwai da ake zargin mambobin kungiyar ne a wasu hare-hare daban-daban da aka kai a jihohin Kogi, Nasarawa da Benuwe, ya kara da cewa an gano wasu sinadirai da hodar iblis wanda nauyinsu ya haura 843kg.

Babafemi ya ce wata kungiya ce a karkashin jagorancin wani mai suna Augustine Emmanuel, mai shekaru 45, ta yi kokarin dakon kayan ta hanyoyin ruwan da ke tsakanin jihohin Edo da Kogi amma abin ya ci tura.

Babafemi ya ce an cafke wadanda ake zargin ne a ranar Litinin “a wata motar Jetty da ke Idah, jihar Kogi, inda wata mota kirar Toyota Avalon lon.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *