fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Hukumar NDLEA ta kwace kwayar Tramadol 34,950 da Diazepam a Jihar Legas

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta ce ta cafke kafso 34,950 na Tramadol da Diazepam da ke cikin garin Legas wadanda za a kai su ga masu tayar da kayar baya a Borno.

Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, a Abuja.

Mista Babafemi ya ce an kama wani matashi dan shekaru 25, Mohammed Isah, da aka dauke shi don yayi safarar magungunan daga Legas zuwa Borno a ranar Talata, a wata tashar mota da ke Agege, Legas.

Ya kara da cewa an cafke wanda ake zargin ne tare da kwayoyi 12, 390 na Tramadol (4.8kg) da kuma na 22,560 na Diazepam (14kg).

Mista Babafemi ya kara da cewa wanda ake zargin ya yi tafiya ne a cikin motar bas da SD Motors ke aiki daga Legas zuwa Kano sannan ya sake daukar wata motar zuwa Maiduguri.

Mista Babafemi ya ce bincike ya nuna cewa kafin kamun Mohammed, Kakali ya yi tafiya daga Lagos zuwa Maiduguri, don jiran isowar kayan.

A karshe Shugaban Hukumar ta NDLEA, Buba Marwa, yana mai jinjina wa jami’an hukumar na jihar ta Legas, saboda taka-tsantsan da suke yi na hana irin wadannan kwayoyi shigowa zuwa Borno, a halin yanzu kasar nan matattarar masu tayar da kayar baya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *