fbpx
Monday, September 27
Shadow

Hukumar NDLEA ta kwato miyagun kwayoyi da kudin su ya kai biliyan N90 cikin watanni biyar – Marwa

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, Birgediya Janar Buba Marwa, a ranar Asabar, ya ce hukumar ta kwato sama da N90bn na haramtattun kwayoyi daga wadanda ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi daga watan Janairu zuwa Mayu 2021.

Marwa ya kuma bayyana cewa an cafke sama da mutane 5,000 da laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi yayin da hukumar ta hukunta sama da 500 a cikin wannan lokacin.

Ya ce yana da mahimmanci a farkar da sanin dukkan ‘yan Najeriya kan bukatar gaggawa da ta ba su goyon ga hukumar ta NDLEA a kokarin ta na ceto kasar daga barazanar cin zarafi da fataucin muggan abubuwa don kare makomar Najeriya.

Tsohon shugaban sojojin ya bayyana hakan a Ibadan, jihar Oyo, yayin gabatar da wani littafi, ‘Nasara a Cin Rashin-nasara’, wanda Birgediya Janar Larinde Laoye (mai ritaya) ya rubuta.

Shugaban na NDLEA ya ci gaba da yin kira ga dukkan shugabanni da masu ruwa da tsaki a duk fadin kasar da su gaggawata kawar da Najeriya daga abin da ya bayyana a matsayin “annobar miyagun kwayoyi”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *