fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Hukumar Sojoji zata kai karar masu yada hotunan gawar Sojojin da aka kashe

Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana rashin jin dadinta kan yanda ake yada hotunan sojojin Najeriya da aka kashe a fagen daga.

 

Sanarwar da kakakin Sojin, Janar Muhammad Yerima ya fitar, yace abin takaici ne yanda ake watsa hotunan gawarwakin sojojin ba kyan gani.

 

Yace a wasu lokutan ma, Iyalan wadannan sojoji suna fara ganin irin wadannan munanan hotunan ne kamin a sanar dasu a hukumance kan mutuwar dangin nasu.

 

Yace daga yanzu, duk wanda ya dake saka hotunan gawarwakin sojojin da aka kashe a fagen daga zasu shiga kotu dashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *